Abokan huldar bankuna na cigaba da nuna bacin ransu sakamakon karancin takardun kudi, A yayin da bankuna da dama, suka takaita yawan kudin da mutum zai iya cira, su kuwa masu POS sun kara cajin da suke yi da kaso 100 bisa 100.
Ziyarar gani da ido da manema labarai suka kai wasu bankuna a Legas da Abuja, sunga yadda abokan huldar bankuna ke shan wahala wajen samun takardun kudi akan injinan cirar kudi na ATM, a yayin da mafi akasarin injinan basa bada kudin.
Akwai dai dan karancin takardun kudi da bankuna ke fuskanta, sakamakon rashin samar masu das u daga babban bankin kasa, lamarin da yasa bankunan suka rage yawan tsabar kudin da mutum zai iya cira akan ATM ko kuma akan kanta.
A wani bangaren kuma, Babban bankin kasa ya dakatar da cajin kudin da ake yiwa abokan huldar bankuna masu ajiyar kudi da yawa, wanda zai kama naira dubu 500 ga masu asusun banki na kashin kai ko kuma naira milyan ukku ga masu asusun ajiya banki ta kanfanoni.