Shugaban kwamitin karbar Mulki na jam'iyyar NNPP Dr Abdullahi Baffa Bichi ne ya jagoranci kai ziyarar gani da Ido zuwa wajen da ake zargin an sayarwa da Abba Ganduje.
Gwamnan jihar Kano mai jiran Gado,Abba Kabir Yusuf Ya ce zai dauki matakin shari’a domin dawo da dukkanin wasu kadarorin gwamnati da ake zargin gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya sayarwa iyalansa.
Da yake jawabi a ranar Laraba, Shugaban kwamitin dawo da kadarorin gwamnati, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin karbar mulki na jam’iyyar NNPP, Dr Abdullahi Baffa Bichi, Ya ce ana zargin an sayar da hukumar nan ta kula da kwangilolin gwamnati dake kan titin state Road, Ga dan gidan gwamnan jihar Kano Abba Ganduje akan kudi naira milyan 10.
Baffa Bichi ya kuma yi zargin cewar , Abba Gandujen ya sayar da wurin akan kudi sama da naira milyan 300, Inda ya baiyana bacin ransa kan irin halaiyyar da gwamnatin mai barin gado take nunawa, ta hanyar cefanar da kadarorin mallakin al’ummar jihar kano.
Duk da wani kokarin na jin ta bakin jami’an gwamnatin jihar Kano mai ci a yanzu domin maida martani kan zargin bai samu nasara ba.
Sai dai idan ba’a manta ba, Gwamna Ganduje ya gargadi zababben gwamnan jihar kano da ya dena azarbabi, inda y a ce ya bari sai an rantsar dashi a matsayin cikakken gwamnan jihar kano kafin daukar irin wannan mataki.