Gwamnan jihar kano, Alhaji Abba Kabir Yusif ya amince da yin karin wasu sabbin nade-nade har guda biyar, akan wasu mukamai daban-daban, a yayin da za’a yi bukin rantsar da mutanen nan bada jimawa ba.
Wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan na kano, Sanusi Bature ya fitar da Asubahin yau, Ta baiyana sunayen mutanen da aka nada kan sabbin mukaman, wanda suka hada da Injinya Garba Ahmed Bichi a matsayin Manajan daraktan Hukumar Samar da Ruwan sha ta jihar Kano.
Sauran sune Dr. Rahila Mukhtar a matsayin Babbar Sakatariyar hukumar kula shirin temakekeniyar lafiya ta jihar kano, Sai Hassan Baba Danffa a matsayin Manajan Darakta na hukumar Gyaran titina ta jihar Kano, KARMA.
Ragowar mutanen sune, Arch. Ibrahim Yakubu a matsayin Manajan darakta na hukumar tsara birane ta jihar Kano KNUPDA, sai kuma Abdulkadir Abdussalam wanda ya zama sabon babban akanta na jihar Kano.