Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Ya amince da nada sabon babban sakataren hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kano, tare da jami’ar gudanarwar hukumar.
Wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Ta baiyana cewar an nada Alhaji Yusuf Lawan a matsayin shugaban hukumar.
Kazalika sanarwar ta baiyana Alhaji Laminu Rabi’u a matsayin bababban sakataren zartarwa na hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kano, Yayin da Sheik Abbas Abubakar Daneji da Shiek Shehi Shehi Maihula da Ambasada Munir Lawan zasu kasance mambobi.
Sauran sune, Shiek Isma'il Mangu da Hajia Aishatu Munir Matawalle da Dr. Sani Ashir a matsayin mambobin hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano.