Zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Ya gargadi shugabannin kananan hukumomi da kuma manyan jami’an gudanar da mulki na kananan hukumomin dasu guji yin amfani da wasu makudan kudade da aka ware da sunan gudanar da zabukan cike gibi da za’a gudanar a wasu wurare a gobe Asabar.
A cikin wata sanarwa ta shawara da zababben gwamnan na kano, Abba Gida Gida ya fitar ta hannun kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa , wanda ya baiyana cewar sun samu cikakkun bayanai kan yin amfani da kudaden.
Ya yi zargin cewar gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin sakin sama da naira milyan sittin-sittin ga kananan hukumomin Doguwa da Nasarawa da Wudilm yayin da wasu kananan hukumomin zasu karbi daruruwan dubunan kudade da sunan gudanar da zaben cike gibin
To sai dai duk da kasancewar har ya zuwa wannan lokaci gwamnatin jihar Kano bata mayar da martani akan wannan sabon zargi da gwamnati mai jiran gado ta yi ba, Sai dai idan ba’a manta ba, A makon jiya ne kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta jihar Kano ALGON ta kalubalanci gwamnati mai jiran gado, inda ta zarge ta da dumama yanayin da ake ciki.
Sanarwar mai dauke dasa hannun shugaban kungiyar Shugabannin kananan hukumomi a nan jihar Kano Baffa Mohammed, Ya musanta zarge-zargen da zababben gwamnan jihar Kanon ya yi, na tuhumar shugabannin kananan hukumomi da karya dokokin tafiyar da kudi.
Ya kara da cewar ba sabon abu bane a rikin samun irin wannan zargi da bashi da tushe balle makama a duk lokacin da aka samu sabuwar gwamnati.