Matukar ba wani sauyi aka samu ba, Nan da 'Yan Sa’oi ne ake saran saukar rukunin farko na ‘yan Najeriyar da suka makale a kasar Sudan a birnin taraiyya Abuja, Kamar yadda Hukumar kula da ‘Yan Najeriya mazauna kasashen ketare NIDCOM ta baiyana.
Shugabar hukumar Abike Dabiri Erewa wadda ta bada wannan tabbaci a daren jiya, Ta ce ofishin jakadancin kasar nan dake Masar ya samu nasarar tsallakar da dukkanin ‘yan Najeriyar da suka makale akan Iyakar Arqeel dake kasar Masar, zuwa cikin kasar, domin dauko su ta cikin jirgi zuwa gida Najeriya.
Rahotanni sun baiyana cewar, Tuni jirgin rundunar sojin sama ta kasa da kuma na Air Peace da aka tura zuwa kasar ke dakon akai masu mutanen domin dauko su zuwa Abuja.
Kazalika ta ce an bayar da kulawa ta musamman ga Dalibai mata, A yayin da ta ce za’a kwashe sauran mutanen da suka makale a kan iyakar Wadi Halfa a safiyar gobe sannan kuma wadanda suke kan iyakar birnin Port Sudan, sune zasu zama na karshe da za’a kwashe, kasancewar a jiya ne suka karasa wajen.