Mai horas da tawagar yan wasan kasar Argentina Lionel Scaloni ya tabbatar da cewa 'yan wasansa sun shirya tsaf domin buga wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya da kasar Croatia a yau.
Gwarzon dan wasan duniya Lionel Messi na kasar Argentina za su kara da fitaccen dan wasan kasar Croatia Luka Modric a wasan kusa da na karshe, yayin da zakarun gasar a shekarar 2018 kasar Faransa za ta kece raini da Morocco a gobe.
Bayan shafe makwanni uku ana gasar a Qatar, kungiyoyi hudu ne suka rage a yayin da ake kan hanyar karkare gasar .
Za'a take wasan ne daga karfe 8 Na dare agogon Najeriya