A yaune Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweramadu tare da mai dakinsa Beatrice zasu san makomarsu, Yayin da wata kotu a Burtaniya zata yanke masu hukunci bayansu samunsu da lefin yunkurin cire sassan Dan adam ,domin yiwa yarsu mai suna Sonia magani.
Gabanin zartar da hukuncin, Wasu daga cikin fitattun ‘yan Najeriya dama kasashen Afrika na cigaba da yin kira ga Kotun data yiwa sanatan sassauci.
Kazalika suma majalisun dokokin kasar nan sunyi irin wannan roko a karshen makon jiya, kamar yadda ita ma wata kungiya ta Ikeoha Mpu ta sake makamancin wannan kira.
Kungiyar ta bukaci kotun data sassautawa jagoran nasu wanda ya kasance dan uwa a gare su, ta hanyar sakinsa batare da gindaya wani sharadi ba.