Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya ce zai bayyana dan takarar da zai marawa baya na shugaban kasa a watan Janairu na shekarar 2023.
Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, ya ce zai kuma yi yakin neman zabe ga dan takarar da ya amince da shi a fadin Najeriya.
"A watan Janairu na shekara mai zuwa, zan nunawa jama'ata wanda za su zaba," in ji Wike.
Da ya ke kaddamar da gadar sama ta goma da gwamnatinsa ta yi a karamar hukumar Obio-Akpor ta Jihar Rivers, yace “saboda haka, duk wadanda suka kasance cikin shakku, suna ta maganganu iri-iri, kuna zagina, ku jira watan janairu yana nan zuwa.
“Ba wai kawai zan sanar da mutanena wadanda za su kadawa kuri’a ba, zan yi famfe daga jiha zuwa jiha domin yakin neman zabe da dalilin da ya sa za su zabi wanda na nuna,”
Bayan zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a watan Mayu inda ya sha kaye, Wike ya shiga takun saka tsakaninsa da Atiku Abubakar kan shugabancin Iyorchia Ayu.
Bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa, Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne ya tsallake Wike inda ya zabi gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa.
Wike tare da wasu gwamnoni hudu na PDP da aka fi sani da G5, sun dage cewa dole ne Ayu haifaffen Jihar Benuwe ya sauka domin a matsayin wani sharadi na goyon bayan tsagin Atiku a zaben 2023.