On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

A Watan Gobe Za'a Fara Rabawa Talakawa Naira Dubu 25

Minista Betta Edu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da biyan naira dubu 25 a kowane wata ga masu karamin karfi dake cikin rijistar bada tallafin tsabar kudi na gwamnatin tarayya.

 

Ministar bada tallafi  da kawar da fatara Betta Edu ce ta sanar da haka a ranar Alhamis, Inda ta ce  shugaban kasar ya umarci ma’aikatar data fara biyan kudin daga watan gobe.

Sanarwar da mashawarcinta a bangaren yada labarai  Rasheed  Zubair ya fitar, Ta Ambato  ministan na baiyana haka a lokacin da  take ganawa da shugaban kungiyar kwadago ta kasa  NLC Joe Ajeoro da kuma takwaransa na TUC  Festus Osifo a Abuja.

Ta yi kira ga kungiyoyin kwadagon dasu temakawa yunkurin gwamnati wajen gaggauta  tattara bayanan masu karamin karfi a kasar nan, domin fara cin gajiyar tsarin.