Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta ce ’yan siyasa masu sayen katin zabe na dindindin daga hannun al’umma da nufin murde zaben 2023 hakan ba zai amfana mu su komai ba domin kuwa yunkurin na su zai tashi a banza.
Kwamishinan INEC na kasa, Festus Okoye ya ce tsarin amfani da BVAS wajen tantance masu kada kuri’a a shekarar 2023, zai gane tare da kawar da bayanan mutanen da ba su ne da asali na katin zaben da ke hannu su ba.
Wasu kungiyoyi masu zaman kansu guda biyu, kungiyar dattawan Arewa da kungiyar SERAP sun yi zargin cewa ‘yan siyasa na sayen katin zabe daga talakawan masu kada kuri’a domin yin magudi a zabe mai zuwa.
Sai dai Okoye ya bayyana shirin a matsayin wanda ba zai taba yin nasara ba, yana mai cewa hukumomin tsaro na da alhakin bibiyar irin wadannan mutane da kuma gurfanar da su gaban kuliya.