Mai Alfarma Sarkin Musulmi , Alhaji Saad Abubakar na III, ya ayyana ranar Juma'a a matsayin ranar 1 ga watan Shawwal na shekarar 1444 bayan Hijira a hukumance, wanda ke nuni da kammala Azumin watan Ramadan na shekara ta 2023.
Bayan tabbatar da ganin watan daga wurare da dama a fadin kasar, Sarkin Musulmin ya bayyana cewa ranar 21 ga Afrilu ce za ta zama ranar farko ta Idin karamar Sallah.
Wannan sanarwar ta nuna kawo karshen azumin bana da akayi kwanaki 29.
Sarkin ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su yi wa kasar nan addu’ar zaman lafiya da hadin kai, inda ya jaddada muhimmancin nuna soyayya da tausayi da gafara a matsayin muhimman halaye ga mabiya addinin Musulunci.