On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Aleksander Ceferine: Mun halaka yunkurin shirya sabuwar gasar nan ta Super League

Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai, Aleksander Ceferine

"Gasar Super League ta mutu, kuma ba za a sake zancen ta ba akalla nan da shekaru 20 masu zuwa".

Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai (UEFA), Aleksander Ceferin ya tabbatar da cewa an binne batun kaddamar da sabuwar gasar nan ta Super League, yana mai cewa zancen ta ba zai sake tashi ba nan da shekaru 20 masu zuwa.

“Bana so na kira gasar da suna Super League, saboda dama can gasar bata ansa wannan lakabi ba,” a cewar shugaban dan kasar Slovenia, bayan babban taron hukumar kwallon kafan ta nahiyar turai da aka gudanar ranar Laraba a birnin Vienna.

A watan Aprilun da ya gabata ne wasu manyan kungiyoyin kwallon kafar nahiyar turai guda 12 suka hada kai domin shirya gasar, sai dai wannan yunkuri ya tunkuyi kasa bayan wasu kwanaki, sakamakon rashin samun goyon bayan yunkurin da yan wasa da kuma magoya bayan kungiyoyin kwallon kafan, har ma da gwamnatocin kasashen da hukumomin wasan kwallon kafa na kasashen da kungiyoyin kwallon kafan ke ciki suka nuna.

Kungiyoyin kwallon kafa guda 9 sun nesan ta kan su daga wannan yunkuri daga baya, sai dai Real Madrid, Barcelona da kuma Juventus sun cigaba da matsa lamba wajen ganin cewa gasar ta tabbata.

Da yake Magana a babban taron hukumar kwallon kafan ta nahiyar turai ranar Laraba, Ceferin, ya bayyana aniyar hukumar na gudanar da garambawul akan dukkanin gasa da hukumar ke shiryawa, yana mai cewa babu yadda za’a yi kungiyoyin guda 3 su samu nasarar busawa gasar ta su ta Super Cup numfashi.

Sai dai ya zuwa yanzu, Ceferin bai bada wata ansa ba, dangane da tambayar da aka yi masa akan hukuncin da hukumar zata dauka akan manyan kungiyoyin guda 3 da suka tubure wajen cigaba da yunkurin kafa gasar ta Super League.

A watan Aprilun da ya gabata ne wani mai shari’a a birnin Madrid na kasar Spaniya, ya sake jaddada hukuncin da wata kotun kasar ta yanke wajen yaye kariya daga fuskantar hukunci da kungiyoyin guda 3 suka nema.

Sai dai ya kara da cewa, “har yanzu batun na gaban kotun kuma dole ne mu mutunta hakan, saboda da haka zamu jira hukuncin kotu na karshe kafin daukar mataki, don ba sauri muke ba”.