Yan bindigar da suka sace wadansu mata Ukku yan uwan juna a jihar Kaduna, wadanda suka hada da wata mai tsohon ciki wadda ta haifi jaririnta a hannun yan bindigar, sunyi barazanar halaka matan da suke tsare dasu.
Kazalika sunyi barazanar halaka jaririn da matar ta Haifa, muddin danginta suka kasa biyan naira milyan 50 nan da kwanaki biyu masu zuwa.
An sace d matan ‘yan uwan juna su ukku a ranar 17 ga watan Yulin bana a gidansu dake Mando a jihar Kaduna, a lokacin da suke kula da lafiyar mahaifiyarsu wadda take fama da rashin lafiya.
Dangin matan da aka sace sun baiyana cewa abunda suka iya hadawa kawo yanzu shine naira milyan 6 da rabi daga cikin makudan kudin da ‘yan bindigar suka neman.
Kazalika shima dan uwan matan mai suna Kabir Yusuf, Lokacin da yake ganawa da manema Labarai a Kaduna, Ya roki gwamnatin jihar da kuma sauran yan kishin kasa dasu temaka masu, domin ceto rayukan bayin Allah.