‘Yan bindiga sun harbe wasu jami’an yansanda guda biyu tare da wani Matashi har lahira, a yayin wani hari da suka kai wata Mahadar kan titi dake karamar hukumar Ahiazu Mbaise ta jihar Imo.
Maharan sun bude wuta batare da kakkautawa ba a lokacin da suka je wurin da jami’an tsaro ke tsayawa domin bincike ababen hawa.
Shaidun gani da ido da suka bukaci a sakaye sunansu sun fadawa manema Labarai cewar, Wani mutum ya gamu da ajalinsa sakamakon wani harsashin bindiga da ya same shi.
A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar yansandan jihar ASP Henry Okoye, Ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce a yanzu haka an fara farautar yan bindigar.