Hukumar ‘yan sandan kasa da kasa ta Interpol ta kama mai sasantawa tsakanin 'Yan Ta'adda da fasinjojin da harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su, Tukur Mamu a filin jirgin sama na birnin Alkahira na kasar Masar, akan hanyarsa ta zuwa kasa mai tsarki domin yin ibadar Umrah.
Ana sa ran Mallam Mamu tare da matansa biyu da kuma wani mutum daya za su isa filin jirgin saman Aminu Kano da yammacin yau Laraba, bayan da jami'an yansandan suka tuso keyarsa.
Duk da cewar malamin yasha musanta cewar yana da wata alaka da 'Yan Bindigar, to sai yace ana yiwa rayuwarsa barazana, sannan kuma ya zargi hukumomin Najeriya da kitsa masa makarkashiyar.
Malam Tukur Mamu shine wanda ke shiga tsakani wajen ganin an sako yan fasinjojin jirgin kasar da yan bindiga suka sace, bayan wani hari da suka kai ma jirgin a bana, inda kowane fasinja ke biyan milyan dari kafin a sako shi, kamar yadda rahotanni suka baiyana.