On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Hukumar DSS Ta Zargi Tukur Mamu Da Temakawa Kungiyoyin Yan Ta'adda

Tukur Mamu

Kotu ta amincewa Hukumar Tsaro ta farin Kaya DSS, ta tsare Mai shiga tsakanin yan ta'adda da fasinjojin jirgin kasar da aka Sace a Kaduna, har nan da kwanaki sittin a matakin farko.

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS  ta yi zargin cewa binciken farko da ta gudanar ya gano wadansu  laifuffuka da ake tuhumar Tukur Mamu dasu, Wanda suka hada da  samar da kayayyaki, da taimakawa kungiyoyin Yan ta'adda na ciki da wajen kasar nan.

A wata takardar Kara da Hukumar ta DSS ta shigar  a gaban mai shari’a Nkeonye Maha na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta kuma yi zargin cewa binciken data fara yi akan Tukur Mamu ya gano cewar Yana daukar nauyin 'yan ta'adda.

A ranar Talata ne kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN,  ya ruwaito cewa Mai Shari’a Maha ya amince da bukatar da lauyan hukumar DSS, Ahmed Magaji ya gabatar, inda ya nemi a kyale Hukumar ta tsare Tukur  Mamu  tsawon kwanaki 60 a matakin farko, har  zuwa lokacin da za'a kammala binciken.

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi zargin cewa binciken farko da ta gudanar ya gano laifuffukan da suka shafi mai samar da kayayyaki, da taimakawa da ayyukan ta’addanci da aka yi wa Tukur Mamu.

Lauyan DSS, ya yi zargin cewa Mamu, Yana amfani da aikinsa na jarida wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci, da kuma bayar da tallafi ga kungiyoyin ta’addanci na cikin gida da kasashen waje.

Jami'an yansandan kasa da kasa ne suka kama shi a birnin Alkahira na kasar Masar a ranar 6 ga watan Satumbar 2022, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiya.

Hukumar ta zaiyana wasu daga cikin kayayyakin da aka samu a gida  da Kuma  ofishin Tukur Mamu da suka hada da dala 151 sai  fam 20 da kudin indiya Rufi Dubu 1 da 530  sai Daya na Saudiya da Dirhami 70 da tsabar kudi miliyan daya da naira dubu dari biyar da shida da Sauran wasu kudade na kasashen waje

Hukumar ta DSS ta kuma yi zargin cewa an samu katinan cirar kudi 16 katunan ATM na bankunan kasar nan da Kuma kasashen waje sai  kwamfutar tafi-da-gidanka guda shida da  wayoyin hannu 24 da fasfo na kasa da kasa guda uku sai wani lasisin mallakar bindiga Daya, da kakin soji guda takwas da Kuma na Sojin ruwa Guda 16 na Wadanda suna daga cikin abubuwa 34 da aka samu a Sumamen da Hukumar ta Kai gidansa