A cewar sanarwar da kungiyar ta fitar, matakan da gwamnati ke dauka
Kungiyar Dattawan Arewa ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi murabus daga kan kujerarsa sakamakon gazawa wajen samar da cikakken tsaro a Najeriya.
Kungiyar ta yi wannan bukata ce ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakinta Dr Hakeem Baba –Ahmed.
Kungiyar Dattawan Arewan ta baiyana bacin ranta dangane da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwashe kimanin shekaru 7 akan karagar mulki, amma har yanzu an gaza magance matsalolin rashin tsaro da suka addabi Najeriya.
A cewar sanarwar da kungiyar ta fitar, matakan da gwamnati ke dauka a halin yanzu basu yi daidai da yanayin magance matsalolin rashin tsaro da ake fuskanta ba.