On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Tsohon Gwamna Dariye Na Shirin Tsayawa Takarar Sanata Bayan Sakinsa Daga Gidan Yari.

Muddin ba'a samu wani sauyi ba, tsohon gwamnan jihar Plateau, Sanata Joshua Dariye, zai bayyana kudirin tsayawa takarar kujerar sanatan Filato ta tsakiya a karkashin jam’iyyar Labour  kamar yadda rahoton Daily Trust ya ruwaito.

A ranar litinin din makon da muke ciki ne ka sallamo Dariye da  tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame, da wasu mutane uku daga gidan yari watanni uku bayan afuwar da majalisar magabata ta Kasa  karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi musu, a ranar 14 ga Afrilun 2022.

Dariye, wanda aka yankewa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 a kan zambar Naira biliyan 1 da milliyan 126, an sake shi bayan kimanin shekaru hudu a gidan yari.

Jaridar daily trust ta rawaito daga majiya mai tushe cewa jam'iyyar LP reshen jihar Filato ta kammala shirye-shiryen karbar tsohon gwamnan  daga Abuja domin karbar fom din takarar sanata na jam’iyyar.