Wani matashi mai kimanin shekaru goma sha - shida da haihuwa mai suna Ibrahim Lawan ya rataye kansa a kauyen Kuki dake Karamar hukumar Bebeji ta nan jihar Kano dake karkashi ikon masarautar Rano.
Jami'in yada labarai na masarautar Nasiru Habu Faragai Shine ya tabbatar da haka ta cikin wata sanarwa da ya aikowa Arewa Radiyo.
Sanarwar ta baiyana cewa Hakimin Bebeji Maji Dadin Rano, Alhaji Tijjani Abdullahi Kuki ya gabatarwa mai Martaba Sarkin Rano, Ambassador kabiru Muhammad Inuwa rahoton faruwar lamarin, Wanda ya faru a ranar sha - hudu ga watan Ogusta da muke ciki, inda aka tarar da matashin ya Rigamu Gidan Gaskiya.
Mai Martaba Sarkin Rano ya bukaci a mika rahoton ga jami'an 'Yan sanda domin fadada bincike.
Haka Zalika an gabatarwa da Sarkin rahoton mutuwar wani Dan achaba Mai suna Abdullahi Isa wanda aka fi sani da Tambai dake kauyen Kodai Chirin a yankin karamar hukumar Bunkure, wanda aka same shi Yashe a gefen hanya an cire masa hannu sannan kuma an yi awun gaba da babur dinsa.
Da yake karbar rahoton, Mai Martaba Sarkin Rano, ya bukaci Hakimai da Dagatai da masu Unguwanni dake masarautar dasu tashi tsaye wajen gudanar da addu'oi domin neman daukin Allah Madaukakin sarki daga samun faruwar irin wadannan matsaloli.