Hukumar Zabe ta kasa mai zaman Kanta INEC, ta yi alkawarin gudanar da zabe mafi inganci a kasar nan fiye da wadanda suka gabata a shekarar 2023.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar jami’an cibiyar nazari kan harkokin dimukuradiyya ta duniya.
Ya ce ganawar ita ce ta farko da INEC ta shirya bayan zaben gwamnan jihar Osun da aka yi ranar Asabar, ya kuma ba da tabbacin cewa za ta inganta nasarorin da ta samu a zabukan da ke tafe.
A nasa jawabin, sakataren harkokin wajen jihar Ohio dake kasar Amurka kuma shugaban tawagar, Frank LaRose ya yabawa hukumar INEC kan kokarinta daban-daban na inganta harkokin zabe a Najeriya.