Shugaban kasar ya baiyana haka ne ta cikin jawabinsa da ya gabatar a dandalin taro na Eagle Square dake Abuja babban birnin taraiyya.
A cewarsa tsarin sauyin takardun kudin da babban bankin kasa ya bijiro dashi ya yi matukar kuntatawa jama’ar kasa.
Ya kuma baiyana cewar a yayin da gwamnatinsa zata yi gyara kan tsarin, jama’a zasu cigaba da amfani da takardun kudin ba tare da samun wata matsala ba.
Bugu da kari ya ce za’a yi sauye-sauye kan tsarin tafiyar da manufofin kudi na kasa.