On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Sufeton 'Yansanda Ya Soki Shirin Samar Da 'Yansandan Jihohi

KAYODE

Babban sufeton yansanda na kasa Kayode Egbetokun, ya nuna rashin amincewarsa da kirkirar ‘yan sandan jihohi, inda ya yi gargadin cewar gwamnonin jihohi zasu mayar dasu yan amshin shata, ta hanyar hada baki da su domin tauye hakkin wani ko kuma bullo da wata matsala ta tsaro.

Sufeton yansandan ya baiyana haka a yayin wani taro da majalisar wakilai ta shirya domin yin muhawara  kan samar da yansandan jihohi  a jiya.

To sai dai kuma gwamnatin tarayya  ta sake jaddada cewa babu ja da baya  kan shirin samar  da  yansandan jihohin.

A yayin taron mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima  ya nanata  kudirin gwamantin shugaban kasa Bola Tinubu na samar da kyakykyawan tsari  wajen kirkirar  yansandan jihohin.