On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Darajar Naira Ta Kara Faduwa A Kasuwar 'Yan Canji

NAIRA DA DALA

Darajar naira ta sake sauka bayan an canzar da ita kan naira dubu 1 da 234 akan kowacce dala daya a jiya, kamar yadda bayanan canjin kudi suka nuna.

Hakan na nufin darajar  nairar  ta sauka  da naira  65 ko kuma kaso 5 da digo 26 cikin 100, kan yadda aka canzar da ita a ranar  juma’a, bisa naira dubu 1 da 169 da kobo 99 akan kowacce dala  daya.

Darajar naira ta samu tagoma shi a ranar Larabar makon jiya  bayan da aka musayar da ita kan naira dubu 1 da naira 72 da kobo 74, wanda  a lokacin yan kasuwar canji sunyi hasashen cewar za’a iya canjar dad ala kasa da naira dubu 1 a karon farko.

To sai dai kuma saukar darajar nairar  ta zo daidai da kalaman da gwamnan babban bankin kasa yemi Cardoso  ya yi,  wanda  y ace  manufar  bankin bas hi  kare darajar naira ba,a  lokacin da aka yi amsa tambaya ka  saukar ma’ajiyar kasar nan ta kasashen waje.